Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiBiyan kuɗi don karɓar beli zai iya jawo hukunci – Rundunar ’yan...

Biyan kuɗi don karɓar beli zai iya jawo hukunci – Rundunar ’yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gargaɗi al’umma da su guji biyan kuɗi domin samun beli ga kansu ko kuma ’yan uwansu, tana mai cewa bayarwa ko karɓar kuɗi don beli na iya jawo hukunci a gaban kotu.

Shugaban sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe a hedikwatar rundunar da ke Abuja, Awuf Jonah, ne ya bayyana hakan yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da aka gudanar a Legas.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an shirya gangamin ne domin wayar da kan mazauna birnin kan hanyoyin kai rahoton jami’an tsaro da suka aikata ba daidai ba, da kuma neman a kare haƙƙoƙinsu.

Jonah ya jaddada cewa karɓar beli a hannun ’yan sanda kyauta ne, don haka bai kamata jami’ai su nemi kuɗi daga waɗanda ke neman beli ba.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su kai rahoton duk wani jami’in da ya nemi kuɗi domin bayar da beli ko kuma ya aikata abin da ya saɓa wa doka, domin a ɗauki matakin da ya dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments