Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da sahihan zaɓuka a Najeriya a shekarar 2027.
Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron tantance shirye-shiryen zaɓukan 2027 da aka gudanar da ma’aikatan hukumar a Jihar Enugu, da ke yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Ya ce hukumar, ƙarƙashin jagorancinsa, tana bin jadawali da ƙa’idojin zaɓe wajen shirye-shiryen da take yi.
Ya ƙara da cewa a riga an samo wasu kayayyakin zaɓe tare da ci gaba da saye da rarraba sauran kayayyakin da ake buƙata.
Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa hukumar tana ƙara samun motocin sufuri domin sauƙaƙa jigilar ma’aikata da kayayyaki.
Haka kuma, an fara horaswa da sake horas da ma’aikata kan sabbin ƙa’idoji da dokokin da aka shigar cikin dokar zaɓe da aka yi wa gyara.
Amupitan ya ce an inganta fasahar sadarwar hukumar tare da ƙarfafa tsaronta.
Ya kuma bayyana cewa INEC ta kafa kwamitoci da suka haɗa da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin taimakawa wajen tabbatar da nasarar gudanar da zaɓukan.
Tun da farko, shugaban INEC na Jihar Enugu, Dr Chukwuemeka Chukwu, ya ce jihar tana da ƙananan hukumomi 17, wuraren rajista 260 da mazaɓu 4,145.
Ya jaddada muhimmancin samar da isassun ma’aikata, kayayyakin sufuri, fasaha da tsaro domin gudanar da zaɓuka cikin nasara.
A taron, wakilai daga jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo sun gabatar da bayanai kan shirye-shiryensu da ƙalubalen da suke fuskanta gabanin zaɓukan 2027.