Akalla mata da mazajensu suka rasu 180 ne suka samu tallafin kuɗi daga Kakakin Majalisar Dokokin Ƙaramar Hukumar Abaji da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, Abdullahi Baba Yahaya, domin rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziki.
Kowace daga cikin matan ta samu naira 10,000, wanda jimillar kuɗin da aka raba ta kai naira miliyan 1.8. An gudanar da rabon tallafin ne a zauren taron majalisar ƙaramar hukumar.
An zaɓi waɗanda suka ci gajiyar tallafin ne daga unguwannin Nuku/Sabon Gari, Central da South-East, inda Yahaya ya ce an yi zaɓin ne a hankali daga gidaje daban-daban domin tallafa wa iyalan da ke cikin mawuyacin hali.
Kakakin majalisar, wanda ke wakiltar mazabar North-East, ya ce shirin ya samo asali ne daga kyakkyawan misalin shugaban ƙaramar hukumar, Abubakar Umar Abdullahi, wanda ya bayyana a matsayin jagoran da ya daɗe yana tallafa wa zawarawa, marayu da sauran masu ƙaramin ƙarfi.
Yahaya ya kuma bayyana cewa ana shirin gudanar da kashi na biyu na shirin tallafin a watan gobe, wanda zai haɗa da ƙarin zawarawa, marayu da sauran masu buƙata. Ya buƙaci sauran kansiloli su yi koyi da wannan mataki, tare da jaddada cewa ɓangaren majalisa da na zartarwa suna aiki tare domin inganta walwalar mazauna ƙaramar hukumar.