Wednesday, October 21, 2026
HomeLabaraiTarihiA rana irin ta yau aka kafa Majalisar Dinkin Duniya a hukumance

A rana irin ta yau aka kafa Majalisar Dinkin Duniya a hukumance

A ranar 24 ga watan Oktoba, 1945, Majalisar Ɗinkin Duniya (United Nations) ta fara aiki a hukumance bayan amincewA rana irin ta yau aka kafa majalisar dinkin Duniya a hukumancea da yarjejeniyar kafuwarta, domin kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

An kafa ta ne bayan gazawar Ƙungiyar Al’ummai (League of Nations) wajen hana barkewar yaƙin a shekarar 1939. Wakilan ƙasashe 50 ne suka tsara yarjejeniyar a birnin San Francisco na Amurka, inda aka sanya hannu a kanta a ranar 26 ga Yuni, 1945.

Da farko, majalisar tana da ƙasashe mambobi 51, amma a yau ta kai 193, tare da hedikwatarta a birnin New York na Amurka.

Manyan manufofinta sun haɗa da sasanta rikice-rikice, kare haƙƙin ɗan Adam, bayar da agajin jin ƙai da inganta haɗin kai tsakanin ƙasashe.

Ana bikin Ranar Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 24 ga Oktoba na kowace shekara, domin tunawa da kafuwarta da kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya a duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments