Wednesday, October 21, 2026
HomeLabaraiKin hana wa Tinubu wa’adi na biyu na iya jefa Najeriya cikin...

Kin hana wa Tinubu wa’adi na biyu na iya jefa Najeriya cikin rikici – tsohon shugaban NAHCON

Tsohon shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi gargaɗin cewa hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa’adi na biyu na iya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.

Tsohon shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi gargaɗin cewa hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa’adi na biyu na iya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da wasu ƙungiyoyin matasa a gidansa da ke Kano, inda ya ce ya kamata a bar Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu, kamar yadda aka bar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa’adi biyu.

Pakistan ya gargaɗi ‘yan siyasa kan ƙin goyon bayan Tinubu saboda yankin da ya fito, yana mai cewa irin wannan siyasa na iya jawo matsaloli a nan gaba tare da kawo cikas ga tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Ya kuma yi ikirarin cewa an samu sauƙin tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, idan aka kwatanta da zamanin Buhari. Haka kuma, ya ce an samu raguwar farashin wasu kayan abinci.

Tsohon shugaban NAHCON ɗin ya ce Tinubu ya gaji matsalolin tsaron Boko Haram da garkuwa da mutane. Ya kuma bayyana cewa buhun shinkafa ya sauka daga naira 120,000 zuwa 57,500, yayin da buhun gero ya ragu daga naira 85,000 zuwa kusan 30,000. Waɗannan alkaluma da ikirarin inganta tsaro sun fito ne daga bayanan da ya bayar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments