Tuesday, October 20, 2026
HomeLabaraiLabaraiJKD TV ta nemi diyyar ₦15m daga Ibrahim Masari da ’yan Sanda

JKD TV ta nemi diyyar ₦15m daga Ibrahim Masari da ’yan Sanda

Gidan talabijin na JKD da ke Kaduna ya garzaya kotu, inda ya shigar da ƙara a kan Ibrahim Kabiru Masari, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, da rundunar ’yan sandan Najeriya.

Kafar ta shigar da ƙarar ne bisa zargin tauye haƙƙin ma’aikatar ta, bayan wani lamari da ya ce ya faru a harabar ofishinsa a watan Satumbar 2026.

A cikin ƙarar da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar 19 ga Oktoba, 2026, tashar tana neman diyyar Naira miliyan 15.

Haka kuma, yana neman kotun ta hana waɗanda ake ƙara sake shiga harabar tashar ba bisa ƙa’ida ba, ko kama ma’aikatansa da ’yan uwansu.

Tashar ta yi zargin cewa a ranar 11 ga Satumbar 2026, wasu jami’an ’yan sanda dauke da makamai sun shiga harabar ofishinsa, inda suka tsare babban manajansa ba tare da umarnin kotu ko wata takardar izini ba.

Daraktar tashar, Aisha Yusuf Mamman, ta ce sun yanke shawarar zuwa kotu ne bayan ƙoƙarin da suka yi na sasanta lamarin bai haifar da ɗa mai ido ba.

Tashar ta kuma bayyana cewa matakan da yake zargin an ɗauka sun saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, duk da cewa har yanzu yana da burin warware matsalar ta hanyar tattaunawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments