Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta kama Faisal Abdulrasheed Maina, ɗan tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho na Najeriya, Abdulrasheed Maina, sannan ta miƙa shi ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa jami’an DSS sun kama Faisal ne a yankin Karsana da ke Abuja, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya dawo Najeriya a ɓoye. An ce yana tsere tun shekarar 2020, bayan ya karya sharuɗɗan beli da aka ba shi.
Faisal na fuskantar tuhume-tuhume guda uku da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da haɗa baki, amma ya gudu daga ƙasar yayin da ake shari’arsa. A shekarar 2021, Mai shari’a Okon Abang ya same shi da laifi, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari.
Kotun ta kuma bayar da umarnin a kama shi duk inda aka same shi a Najeriya domin ya fara zaman gidan yari, tare da umartar gwamnati ta bi hanyoyin doka wajen dawo da shi ƙasar idan aka same shi a ƙasashen waje.
Ana sa ran miƙa Faisal ga EFCC zai taimaka wajen aiwatar da hukuncin kotun, domin ya fara zaman gidan yarin da aka yanke masa.