Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciKamfanin Simintin Dangote da da ke Obajana ya bayar da tallafin karatu...

Kamfanin Simintin Dangote da da ke Obajana ya bayar da tallafin karatu ga ɗalibai 80

Kamfanin Dangote Cement Plc, reshen Obajana, ya bayar da tallafin karatu da na bunƙasa sana’o’i ga ɗalibai, manoma da ’yan kasuwa mata a al’ummar Jakura da ke jihar Kogi, domin inganta rayuwar mazauna yankin.

Kamfanin Dangote Cement Plc, reshen Obajana, ya bayar da tallafin karatu da na bunƙasa sana’o’i ga ɗalibai, manoma da ’yan kasuwa mata a al’ummar Jakura da ke jihar Kogi, domin inganta rayuwar mazauna yankin.

Daraktan kamfanin na Obajana, Injiniya Azad Nawabuddin, wanda shugaban sashen hulɗa da al’umma, Prince Ademola Adeyemi, ya wakilta, ya ce shirin na daga cikin cika alƙawuran da kamfanin ya ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar bunƙasa al’umma.

A cewarsa, ɗalibai 20 na manyan makarantu da wasu 60 na sakandare sun samu tallafin kuɗi na karatu da ya kai miliyoyin naira. Haka kuma, manoma 20 sun samu kayan aikin gona da tallafin kuɗi domin haɓaka noma da samar da abinci.

Haka kuma, ’yan kasuwa mata 20 sun samu jari da tallafin bunƙasa sana’o’insu, domin ƙarfafa tattalin arzikinsu da ƙara samun kuɗin shiga ga iyalansu.

Shugaban kwamitin yarjejeniyar bunƙasa al’umma ta Jakura, Chief Bonibade Ajiboye, ya yaba wa kamfanin bisa cika alƙawuransa, yana mai cewa aikin samar da wutar lantarki a yankin na dab da kammaluwa duk da matsalolin tsaro.

Shi ma Obaron Jakura, Oba Usman Adoga Ajibola, ya gode wa kamfanin da Alhaji Aliko Dangote bisa gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa al’umma, tare da yin kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments