Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC-PCC) ya soki matakin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30.
Ya bayyana cewa matakin wani rangwame ne na wucin gadi gabanin babban zaɓen 2027.
Kwamitin ya mayar da martani ne kan sanarwar da Ministan Kuɗi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ya yi cewa ’yan Najeriya za su amfana da ragin farashin man fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon wata guda.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Alhamis, ya ce matakin ya nuna cewa manufofin tattalin arzikin gwamnati sun jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin hali.
Ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta shafe sama da shekaru uku tana aiwatar da manufofin tattalin arziki da suka ƙara wa ’yan Najeriya wahala, ciki har da cire tallafin man fetur da faduwar darajar naira.
Ologbondiyan ya kuma yi tambaya kan abin da zai faru bayan karewar kwanaki 30, yana mai cewa farashin man fetur na iya komawa sama da N1,400 kan kowace lita.
Ya bayyana matakin a matsayin wani shiri na siyasa maimakon ingantacciyar manufar tattalin arziki, yana mai cewa hakan ya shafi miliyoyin iyalai da ke fama da tsadar kayan masarufi, ƙananan ‘yan kasuwa da masu sufuri.ADC-PCC ya kuma yaba wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan ci gaba da sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, musamman cire tallafin man fetur ba tare da samar da isassun matakan kariya ga al’umma ba.
Kwamitin ya ce rage farashin man fetur na wucin gadi ya ƙara nuna cewa Atiku ya yi daidai wajen yin kira da a samar da man fetur a farashi mai sauƙi ga ’yan Najeriya.
A cewar kwamitin, gwamnatin tarayya ta fara fahimtar cewa cire tallafin man fetur ba tare da samar da isassun hanyoyin rage radadin matsalar ba babban kuskure ne na manufofi.
Ologbondiyan ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka bar ’yan Najeriya suna fuskantar tsadar man fetur na sama da kwanaki 800, alhali gwamnati na da damar rage musu wannan nauyi.
Ya ce matakin ya nuna cewa gwamnati tana da damar sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya, amma ta zaɓi yin hakan ne a lokacin da zaɓe ke gabatowa.
Ya ƙara da cewa rage farashin man fetur na ɗan lokaci ba zai kawar da matsalolin da ’yan Najeriya suka fuskanta ba, waɗanda suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, yunwa, rashin aikin yi, raguwar ƙarfin saye da matsalar tsaro.
ADC-PCC ya buƙaci ’yan Najeriya su kasance masu taka-tsantsan tare da guje wa yaudarar da za ta iya zuwa ta hanyar rangwamen wucin gadi, yana mai bayyana ADC a matsayin wata mafitar siyasa ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar.