Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamnan Kano ya umarci ma’aikatan da suka kai lokacin ritaya su ajiye...

Gwamnan Kano ya umarci ma’aikatan da suka kai lokacin ritaya su ajiye aiki

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci dukkan ma’aikatan gwamnati da suka kai lokacin yin ritaya, ko dai saboda cikar shekarun ritaya ko kuma tsawon lokacin da suka yi suna aiki, da su ajiye ayyukansu nan take.

Gwamnatin ta kuma umarci ma’aikatan da abin ya shafa su miƙa dukkan takardun gwamnati, kadarori da sauran ayyukan da ke hannunsu ga jami’an da aka ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukan.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Babban Sakataren da ke kula da Ma’aikata da Tsarin Aiki, Abba A. Danguguwa, ya fitar a madadin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano a ranar 6 ga Oktoba, 2026.

Sanarwar ta ce ci gaba da aiki bayan cikar lokacin ritaya ya saɓa wa dokokin aikin gwamnati na Jihar Kano da kuma sauran ƙa’idojin da suka shafi ma’aikata.

Ta kuma umarci Manyan Sakatarori, shugabannin hukumomi da Daraktocin Gudanarwa da Kula da Ma’aikata da su tabbatar da aiwatar da umarnin nan take.

Gwamnatin ta yi gargadin cewa duk wani jami’in da aka samu yana taimakawa ko amincewa da ci gaba da aikin ma’aikacin da ya kai lokacin ritaya zai fuskanci matakin ladabtarwa bisa tanadin dokokin aikin gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments