Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamna Abba Yusuf ya sasanta Barau da Bichi bayan rikicin siyasa

Gwamna Abba Yusuf ya sasanta Barau da Bichi bayan rikicin siyasa

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, bayan rikicin siyasar da ya shiga tsakaninsu.

Taron sulhun ya gudana ne a Abuja da safiyar Laraba, inda ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu. Taron ya bai wa shugabannin biyu damar tattauna matsalolin da suka raba su tare da duba hanyoyin haɗa kai domin amfanin jam’iyyar APC a Kano.

Gwamna Abba Yusuf ya yi kira ga Sanata Barau, Hon. Bichi da magoya bayansu da su ajiye duk wani saɓani a gefe, tare da mayar da hankali kan haɗin kai domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Gwamnan ya ce bambance-bambancen ra’ayi na daga cikin tsarin siyasa, amma bai kamata ya zama sanadin raba kan jam’iyya ko kawo cikas ga ci gabanta ba. Ya kuma gargadi magoya bayan shugabannin biyu da su guji zagi, ɓatanci da kalaman da za su iya ƙara rura wutar rikici.

“Henceforth, I do not expect any of your supporters to come out and abuse one another. We must put a stop to this unnecessary distractions,” in ji Gwamna Abba Yusuf.

Sanata Barau Jibrin da Hon. Abubakar Kabir Bichi sun bayyana godiyarsu ga Gwamnan kan shiga tsakani da ya yi, tare da yin kira ga magoya bayansu da su guji duk wani abu da zai sake rura rikicin cikin gida na APC a Kano.

Sun kuma tabbatar da ci gaba da goyon bayansu da biyayyarsu ga jam’iyyar, yayin da Gwamna Abba Yusuf ya ce yana da yakinin sulhun zai ƙara haɗa kan ‘yan APC tare da ƙarfafa damar jam’iyyar a zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments