Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta kama mutane 13 da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyoyin asiri a wasu samame daban-daban da jami’anta suka gudanar.
Rundunar ta ce an kuma ƙwato bindigogi, harsasai, tsafi, kayan da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyoyin asiri, miyagun ƙwayoyi da wasu makamai masu haɗari, tare da wata mota da aka ruwaito an sace.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, inda ya ce jami’an sashen ’yan sandan Okpoko sun kai samame a ranar 30 ga Satumba, bayan samun sahihan bayanan sirri.
A cewar sanarwar, samamen ya kai jami’an zuwa wani wuri da ake zargin ɓoyayyen sansanin masu aikata laifuka ne, wanda ke kusa da Kasuwar Coca-Cola da ke Okpoko.
Rundunar ta ce bayanan da wani daga cikin waɗanda aka kama ya bayar sun taimaka wajen gano wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar.
Rundunar ta ƙara da cewa tana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin, domin gano ƙarin bayanai da kuma gurfanar da waɗanda ake samu da laifi a gaban kotu.