Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaWike ya mayar wa Atiku martani kan karɓar kuɗin ’yan siyasa lokacin...

Wike ya mayar wa Atiku martani kan karɓar kuɗin ’yan siyasa lokacin zaɓe

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya yi game da karɓar kuɗin da ’yan siyasa ke rabawa yayin lokacin zaɓe.

Atiku ya bayyana cewa ya kamata ’yan Najeriya su karɓi duk wani kuɗi da ’yan jam’iyyar da ke mulki za su ba su, yana mai cewa kuɗin na gwamnati ne ko na jama’a, kuma bai kamata a bar shi ya koma hannun wasu kaɗan ba.

Sai dai Wike ya ce ya yi mamakin kalaman Atiku, musamman yadda ya danganta kuɗin da ’yan siyasa ke rabawa da kuɗin sata, sannan kuma yake magana kan yaƙi da cin hanci da rashawa.

Da yake mayar da martani, Wike ya ce: “Lokacin da na ga Atiku a talabijin jiya yana cewa ’yan Najeriya su karɓi duk wani kuɗin da mutanen jam’iyyar da ke mulki za su ba su, domin kuɗin sata ne, sai na ce, haa, Atiku yanzu ya zama mai yaƙi da cin hanci?”

Wike ya kuma koma kan tsohon rikicin siyasa tsakanin Atiku da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, inda ya yi nuni da kalaman da Obasanjo ya taɓa yi kan zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa.

Ministan ya ce Obasanjo ya taɓa bayyana nadamarsa kan naɗa Atiku a matsayin mataimakinsa tare da yin wasu zarge-zarge a kansa.

Kalaman Wike na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun muhawara tsakanin manyan ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments