Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce adadin mutanen da suka yi rajistar zaɓe a Najeriya ya haura miliyan 103, gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja, yayin wani taron ƙwararru da aka shirya wa manyan editoci, wanda Ƙungiyar Editocin Najeriya (NGE) ta shirya tare da haɗin gwiwar hukumar.
Ya ce mutane 2,611,266 ne suka yi rajista a kashi na farko na CVR, yayin da aka samu 4,121,835 a kashi na biyu, sannan aka samu 3,867,997 a kashi na uku.