’Yan bindiga sun bai wa iyayen ’yan bautar ƙasa 20 da aka yi garkuwa da su a kan hanyarsu ta zuwa sansanin horaswa a Jihar Abia wa’adin awa 24 domin biyan kuɗin fansa.
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun tuntubi iyayen ta amfani da wayoyin ’ya’yansu, inda suka buƙaci a biya kuɗin fansa tare da barazanar cutar da waɗanda suka yi garkuwa da su idan ba a biya kuɗin cikin wa’adin da suka sanya ba.
Iyayen waɗanda aka sace sun kai ƙorafinsu ga Sarkin Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbenga Abimbola, domin neman taimako wajen ganin an kuɓutar da ’ya’yansu.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce ya tuntuɓi takwaransa na Jihar Imo, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya.