Jami’an sojojin Najeriya sun fara karɓar sabon albashin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi, wanda ƙarin sa ya bambanta daga kashi 30% – 80%, gwargwadon matsayin kowane jami’i.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ne ya bayyana hakan, yayin da Kakakin Rundunar Sojin Ƙasa, Onyechi Anele, da wani jami’i daga Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) suka tabbatar da fara biyan sabon albashin.
A watan Agusta ne Tinubu ya amince da sabon tsarin albashin, wanda ya shafi kusan jami’an rundunonin sojin ƙasar 250,000. Tsarin ya fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2026.
A sabon tsarin, jami’an da ke sama da matsayin Kanal, ciki har da Birgediya-Janar, Manjo-Janar, Laftanar-Janar da Janar, za su samu ƙarin kashi 30 cikin 100.
Waɗanda suke daga matsayin Kanal zuwa Warrant Officer za su samu ƙarin kashi 50, yayin da sojojin daga Private zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin kashi 80.
Sabon tsarin zai kuma ƙara yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa wajen biyan albashin jami’an rundunonin sojin ƙasar a shekara, daga N660bn zuwa N924bn.
A cewar Dada Olusegun, fara karɓar sabon albashin na daga cikin matakan da ake sa ran za su taimaka wajen ƙarfafa gwiwar jami’an soji, musamman waɗanda ke gudanar da ayyuka a fagen daga.