Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciDangote zai raba wa dalibai hannun jarin matatarsa kyauta

Dangote zai raba wa dalibai hannun jarin matatarsa kyauta

Gidauniyar Aliko Dangote ta ƙaddamar da wani shiri da zai bai wa ɗaliban manyan makarantu a Najeriya damar samun ƙarin hannun jarin Matatar Dangote guda 10 kyauta, bayan sun sayi aƙalla hannun jari 10 da kansu.

Shirin ya shafi ɗaliban manyan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da aka amince da su, waɗanda shekarunsu suka kai 18 ko sama da haka.

Manufar shirin ita ce ƙara wayar da kan matasa kan harkokin kuɗi, zuba jari da kuma mallakar kadarori domin samun arziƙi na dogon lokaci.

A cewar Gidauniyar, ɗaliban da suka cancanta za su fara ne da kammala aikin tantancewa ta dandalin da aka ware.

Bayan kammala tantancewar, ɗalibin zai iya shiga tsarin sayen hannun jarin Matatar Dangote, inda ake buƙatar ya sayi aƙalla hannun jari 10.

Bayan ɗalibin ya cika waɗannan sharuɗɗa, Gidauniyar za ta ɗauki nauyin sayen masa ƙarin hannun jari 10, ba tare da ɗalibin ya sake biyan kuɗin waɗannan hannayen jarin ba.

Shugaban Gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce manufar shirin ita ce bai wa matasa damar fahimtar yadda zuba jari da mallakar kadarori ke aiki tun suna kanana.

Ya bayyana cewa fahimtar harkokin zuba jari tun da wuri na iya taimaka wa matasa wajen yanke shawarar kuɗi bisa fahimta, tare da ƙarfafa su su shiga harkokin tattalin arziki.

Gidauniyar ta kuma bayyana cewa ba za a iya amfani da wannan shiri wajen sayen hannun jari a madadin wani mutum ko wani kamfanin Dangote, ko kuma wani kamfani daban ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments