Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaBa zan yi hutu a kasashen waje ba idan na zama Shugaban...

Ba zan yi hutu a kasashen waje ba idan na zama Shugaban kasa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (NDC), Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a 2027, ba zai riƙa yin hutunsa a ƙasashen waje ba.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, yayin da Najeriya ke bikin cikar shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Ya ce a maimakon zuwa ƙasashen waje domin hutu, zai riƙa ziyartar jihohin Najeriya domin samun damar ganin ƙasar da idonsa, sauraron al’umma da kuma fahimtar ƙalubalen da suke fuskanta.

Obi ya ce zai yi hutunsa a jihohi daban-daban kamar Zamfara, Borno, Kwara, Ebonyi, Edo da Ekiti, tare da sauran sassan ƙasar.

A cewarsa, hakan zai ba shi damar samun ƙarin fahimta kan rayuwar ’yan Najeriya da kuma matsalolin da suke fuskanta a yankuna daban-daban.

Obi ya kuma bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya ce za su kasance cikin abubuwan da zai mayar da hankali a kansu idan ya samu damar jagorantar ƙasar, ciki har da tsaro, ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa tattalin arziki.

Ya ce burinsa shi ne ganin an gina Najeriya inda yara za su samu damar zuwa makaranta, manoma su samu damar komawa gonakinsu cikin tsaro, sannan matasa su samu ayyukan yi da damar bunƙasa rayuwarsu.

Ya kuma yi alkawarin gudanar da gwamnati bisa gaskiya, riƙon amana da adalci, tare da tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen amfanin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments