Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiHakkinmu ne mu sake zaben Tinubu ya kammala shekara 8 a mulkin...

Hakkinmu ne mu sake zaben Tinubu ya kammala shekara 8 a mulkin Najeriya – Gwamnan Kano

Gwamnan Kano ya ce hakan zai ba Kudu damar kammala wa’adin shekaru takwas kafin mulki ya koma Arewa a 2031

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, domin ya kammala abin da ya bayyana a matsayin tsarin raba madafun iko tsakanin Arewa da Kudu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Fadar Gwamnatin Kano, yayin bikin fara rabon motoci 50 da Babban Hafsan Niger Delta, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayar domin tallafa wa ayyukan wayar da kan jama’a na jam’iyyar APC gabanin zaben 2027.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya ce Arewa ta kammala wa’adin shekaru takwas na mulki a karkashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023, don haka ya kamata a bar Kudu ta kammala nata shekaru takwas a karkashin Tinubu kafin mulki ya koma Arewa a 2031.

Ya ce Tinubu ya shafe kusan shekaru uku da rabi a kan mulki, kuma ya kamata a sake zabensa domin ya kammala wa’adin shekaru takwas da tsarin rabon mulki ya tanada.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shafe shekaru uku da rabi yana yi wa Najeriya hidima. Yanzu muna tunkarar wani zabe. Saboda haka, hakkinmu ne a matsayinmu na ’yan Najeriya mu amince cewa ya kamata a sake zaben Shugaban kasar na wani wa’adin mulki,” in ji shi.

Gwamnan ya ce idan aka kammala wa’adin na biyu na Tinubu a 2031, Kudu za ta kai shekaru takwas a kan karagar mulki, sannan damar shugabancin kasar za ta koma Arewa.

“A karshen wannan wa’adi, mulki zai dawo Arewa. Kuma Allah ne kadai Ya san wanda zai zama Shugaban Najeriya,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Arewa, musamman na yankin Arewa maso Yamma, da su goyi bayan sake zaben Tinubu, yana cewa:

“Dole mu yi hakuri. Allah Ya kai mu 2031.”

Haka kuma, Gwamnan ya bukaci ’yan siyasa da magoya bayansu su tabbatar da cewa yakin neman zaben 2027 ya kasance cikin zaman lafiya kuma ya mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen raya kasa, maimakon bata sunan abokan hamayya.

Ya ce ya kamata ’yan takara su gabatar da abubuwan da suka cimma da kuma abin da suke shirin yi idan aka zabe su, domin yakin neman zabe ya fi karkata ga ci gaban kasa da jin dadin jama’a.

Gwamnan ya ce Kano na ci gaba da goyon bayan manufofin gwamnatin tarayya, musamman a bangaren samar da ababen more rayuwa da bunkasa jarin dan Adam. Ya kuma gode wa Tompolo kan gudummawar motocin 50, yana mai cewa za a rarraba su domin tallafa wa tsarin APC da ayyukan wayar da kan jama’a a kananan hukumomin Kano 44.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments