Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na aiki wajen gyara kura-kurai da kuma damar da gwamnatocin da suka gabata suka rasa, yana mai cewa Najeriya na kan hanyar samun ci gaba.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, yayin wata addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Shugaban ya bukaci ’yan Najeriya da kada su yanke ƙauna, yana mai cewa zaman lafiya da ci gaba na dawowa ƙasar yayin da dimokuraɗiyya ke ci gaba.
Ya kuma ce ya kamata ’yan ƙasa su duba manufofin gwamnatinsa da ƙoƙarinta na gyara kura-kuran da aka tara a baya.
Tinubu ya bayyana tafiyar Najeriya tun bayan samun ’yancin kai a matsayin wadda ta haɗa da ƙalubale da kuma damammaki, yana mai cewa cikar ƙasar shekaru 66 na nuna cewa ta kai matsayin balaga.
A cikin saƙon da Abbas ya isar, Tinubu ya ce Najeriya na kan hanyar da ta dace kuma akwai fata na samun ingantaccen ci gaba.
Ya kuma nemi a ba gwamnatinsa ƙarin dama domin ta kammala ayyukan da ta fara.