Kotun Tarayya da ke zama a Jihar Gombe ta umarci Jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a jihar.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis yayin da take yanke hukunci kan ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar yadda Farfesa Isa Ali Pantami ya samu tikitin jam’iyyar na takarar gwamna.
Garry ya ƙalubalanci fitowar Pantami bayan da PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni, 2026.
Ya yi zargin cewa jam’iyyar ba ta gudanar da zaɓen fidda gwani da doka da ƙa’idojin jam’iyyar suka tanada ba kafin ta bayyana Pantami a matsayin ɗan takara.
Pantami, wanda tsohon ɗan takarar jam’iyyar APC ne, ya koma PDP ne bayan APC ta amince da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar da aka cimma matsaya a kansa.
Daga bisani, Pantami ya samu tikitin PDP ta hanyar amincewar ’yan jam’iyyar baki ɗaya a wani zaɓen fidda gwani na takarar gwamna da aka gudanar a watan Mayu.
Sai dai a hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Mohammed ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe da suka dace.
Hukuncin kotun ya soke fitowar Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamna, tare da umartar jam’iyyar da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani.
Ana sa ran ƙarin bayani kan hukuncin da matakan da jam’iyyar za ta ɗauka zai biyo baya.