Fadar White House ta ƙaddamar da wata sabuwar tashar talabijin ta yanar gizo mai suna Trump TV, wadda gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ce za ta riƙa samar da muhimman bayanai ga jama’a.
Ƙaddamar da tashar ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan wasu manyan kafafen talabijin na Amurka sun dakatar da ɗaukar rahotannin kai tsaye daga fadar, domin nuna rashin amincewa da matakin da Trump ya ɗauka na hana wasu kafafen yaɗa labarai shiga White House.
Trump ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da yada labaran ƙarya game da gwamnatinsa.
A wata sanarwa, gwamnatin Trump ta ce damar shiga White House gata ce, ba haƙƙi ba, tana mai cewa babu wani shugaban ƙasa da doka ta tilasta masa karɓar wata kafar yaɗa labarai da take adawa da gwamnatinsa.