Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da shirin sufuri na CNG kyauta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, yana mai cewa irin wannan tsari na taimakawa wajen rage wa al’umma nauyin kuɗin sufuri.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce motocin bas 100 masu amfani da iskar CNG da jihar ta girke sun yi jigilar fasinjoji kusan miliyan 3.2 a shekarar farko ta fara aiki.
A cewarsa, shirin ya taimaka wa mazauna Kaduna wajen rage kashe kuɗin sufuri da sama da naira biliyan 3.5, lamarin da ya bayyana amfanin shirin ga al’umma.