Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta musanta rahotannin da ke zargin an karkatar da kujerun mahajjata 5,000 da aka ware wa aikin Hajjin 2027, tana mai cewa zargin ba shi da tushe.
NAHCON ta ce adadin kujerun da Najeriya ta samu na Hajjin 2027 ya kai 50,000, inda aka ware 35,000 ga jihohi da Abuja, sannan 15,000 ga kamfanonin yawon buɗe ido na Hajji masu lasisi.
Hukumar ta ce kujerun kamfanoni 15,000 an raba su ne ga kamfanoni masu lasisi da ke aiki karkashin manyan kamfanoni bakwai da aka amince da su, bisa ka’idojin Najeriya da na hukumomin Saudiyya.
Ta kuma ce babu wata hujja da ta nuna cewa rabon kujerun 5,000 ya saba wa dokokin Saudiyya, ka’idojin NAHCON ko sauran manufofin gudanar da aikin Hajji.
NAHCON ta ce cece-kucen ya fi alaƙa da gasa tsakanin kamfanonin da ke neman samun kaso daga cikin kujerun da ake da su. Ta kuma ce wasu masu ruwa da tsaki ya kamata su fi mayar da hankali wajen cika sharuddan rajista da ɗora bayanan mahajjata.
Hukumar ta ce ranar 26 ga Satumba 2026 ce wa’adin da hukumomin Saudiyya suka sanya na ɗora bayanan rajista da na’urar tantancewar mahajjata a shafin Nusuk-Masar, kuma NAHCON ba ta da ikon tsawaita wa’adin.
Ta gargadi kamfanonin da suka gaza cika sharuddan da za su iya fuskantar hukunci, ciki har da dakatar da lasisi ko soke shi. Ta kuma shawarci mahajjatan da suka yi rajista ta kamfanoni masu zaman kansu su tabbatar da cewa an ɗora bayanansu kafin wa’adin.