Hukumar ajiya da gyaran hali ta Najeriya (NCoS), tare da hadin gwiwar kungiyar PRAWA, da tallafin Shirin Raya Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) da kungiyar RoLAC, ta bai wa mutane takwas da ke karkashin tsarin zaman hukunci a gida a Jihar Kano kayan fara sana’a da na bukatun yau da kullum.
Jami’in Hulda da Jama’a na NCoS a Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nasarawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce an zabi wadanda suka amfana da kayan ne domin karfafa musu tattalin arziki da taimaka musu wajen komawa cikin al’umma, dogaro da kansu da kuma bayar da gudummawa mai amfani ga al’umma bayan samun horo kan sana’o’i da kasuwanci daban-daban.
Kayayyakin da aka raba sun hada da injinan dinki na Butterfly guda uku, akwatin kayan aikin kafinta, kwalin kajin ‘yan tsaki tare da buhunan abinci guda biyu, injin gyaran tsaki guda daya da akwatunan kayan aikin girka tirela guda biyu.
Da yake wakiltar Shugaban NCoS na Kasa, CGC Sylvester Ndidi Nwakuche, Mataimakin Shugaban Hukumar na Kasa mai kula da Sashen Masu Zaman Hukunci a Gida, Ibrahim N. Idris, Esq., ya bukaci wadanda suka amfana da kayan da su yi amfani da su yadda ya kamata.
Ya ce Sashen Kano zai ci gaba da sa ido tare da tallafa musu yayin da suke amfani da kwarewar da suka samu wajen gudanar da sana’o’insu, tare da karfafa musu gwiwa su zama masu dogaro da kansu da kuma masu daukar nauyin iyalansu da al’umma.
DCG Idris ya bayyana cewa shirin ya yi daidai da manufofin Dokar Hukumar Ajiya da Gyaran Hali ta Najeriya ta shekarar 2019, musamman wajen gyaran hali, sake fasalin rayuwa, komawa cikin al’umma da karfafa tattalin arzikin mutanen da ke karkashin sa ido na hukumar.
Ya kuma gode wa PRAWA, UNDP, RoLAC da sauran abokan huldar hukumar bisa tallafawa matakan gyaran hali ba tare da tsare mutum a gidan yari ba.
A nasa jawabin, Shugaban NCoS na Jihar Kano, CC Ahmed Yusuf Lakpene, ya tarbi Shugabar PRAWA, Farfesa Uju Agomoh, da tawagarta zuwa rundunar.
Ya gode wa PRAWA bisa zabar Kano a matsayin daya daga cikin wuraren da za su amfana da shirin, tare da yaba wa Sashen Masu Zaman Hukunci a Gida bisa kokarin ganin an samu nasarar aiwatar da shirin.
Ita ma Shugabar PRAWA, Farfesa Uju Agomoh, ta yabawa NCoS bisa hadin gwiwar da take bayarwa wajen aiwatar da matakan gyaran hali ba tare da tsare mutum ba a Najeriya.
Ta bukaci wadanda suka amfana da kayan da su yi amfani da su wajen kafa sana’o’i masu dorewa, tare da tabbatar da ingancin ayyukansu domin samun amincewar jama’a da jawo kwastomomi.
Ta kuma jaddada muhimmancin aiki tukuru, daukar nauyi da jajircewa wajen samun nasarar komawa cikin al’umma.
Raba kayan sana’ar na daga cikin kokarin NCoS da abokan huldarta na karfafa gyaran hali, dogaro da kai da kuma taimaka wa mutanen da ke karkashin tsarin zaman hukunci a gida wajen sake komawa cikin al’umma.