Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Neja ta dakatar da kwamandan NSCDC bayan mutuwar masu haƙar ma’adinai...

Gwamnatin Neja ta dakatar da kwamandan NSCDC bayan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) na Jihar Neja, Suberu Aniviye, bayan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 da jami’an hukumar suka kama bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayar da umarnin dakatar da kwamandan a ranar Juma’a, tare da sanar da cewa an fara gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar mutanen.

A cewar gwamnatin, Aniviye zai ci gaba da kasancewa cikin dakatarwa har sai an kammala binciken.

Masu haƙar ma’adinan dai an kama su ne a ƙauyukan M.I. Wushishi da Lukotoba a lokacin samamen da NSCDC ta gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026.

Kwamandan ya ce daga baya an samu wasu daga cikin waɗanda aka kama sun mutu a sanyin safiyar Alhamis bayan wani abin da ake zargin tashin gobara ne.

Biyo bayan lamarin, gwamnatin Jihar Neja ta soke gangamin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa a Minna ranar Asabar, 19 ga Satumba.

Ministan Harkokin Cikin Gida ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’an da ke gudanar da bincike damar gano gaskiyar lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments