Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamnan Neja ya ce gonarsa na biyan mafi ƙarancin albashi N500,000

Gwamnan Neja ya ce gonarsa na biyan mafi ƙarancin albashi N500,000

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce gonarsa na biyan ma’aikatan da suka kammala karatu mafi ƙarancin albashin N500,000 a kowane wata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Legas yayin bikin buɗe taron FirstBank Agric & Export Expo 2026, mai taken “Daga gona zuwa kasuwannin duniya: Gina sarkar darajar fitar da kayayyakin Najeriya zuwa ƙasashen waje.”

Bago, wanda ya bayyana kansa a matsayin manomi, ya jaddada cewa harkar noma, musamman kiwon dabbobi, na da babbar damar samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce albashin da ake bai wa ma’aikata a gonarsa ya fi abin da wasu ma’aikatan gwamnati ke samu.

“A gonarmu, muna biyan wanda ya kammala karatu mafi ƙarancin N500,000 a wata,” in ji Bago.

Ya kuma tambayi irin albashin da ma’aikatan gwamnati da na FirstBank ke samu, yana mai cewa hakan na nuna irin damar da kamfanonin noma masu zaman kansu ke da ita wajen samar da ayyukan yi masu kyau.

Bago ya yi tsokacin cewa gonarsa za ta iya ɗaukar ma’aikatan FirstBank da ke samun albashi ƙasa da N500,000 a wata.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ƙarin masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu da su shiga harkar noma domin bunƙasa fannin da samar da ayyukan yi.

Ya ce dogaro da shigo da abinci daga ƙasashen waje ba zai dore ba, don haka ya kamata a samar da tsari na ƙasa da zai ba da fifiko ga noman cikin gida.

Bago ya bayyana cewa samun wadatar abinci a Najeriya da dogaro da abin da ake nomawa a cikin gida abu ne mai matuƙar muhimmanci.

A cewarsa, Najeriya ta shigo da abinci daga ƙasashen waje da ya kai sama da dala biliyan uku a bana, kuma adadin na iya kaiwa dala biliyan huɗu kafin ƙarshen shekara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments