Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce harkokin kasuwanci da bunƙasa fasaha na da muhimmiyar rawa wajen rage talauci, samar da guraben tattalin arziƙi da inganta rayuwar jama’a.
Fintiri ya bayyana hakan ne yayin da ya ƙaddamar da shugaban da mambobin kwamitin gudanar da Adamawa State College of Technology, Innovation and Entrepreneurship Studies, Gulak, a gidan gwamnati da ke Yola ranar Juma’a.
Gwamnan ya ce kafa cibiyoyin da suka shafi fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci zai taimaka wajen bai wa matasa ƙwarewar aiki, ƙarfafa dogaro da kai da kuma shirya su domin shiga harkokin tattalin arziƙin zamani.
Ya bukaci mambobin kwamitin da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen bai wa kwalejin jagoranci mai inganci, tare da mayar da ita cibiyar bunƙasa fasaha da samar da ƙwararrun matasa masu iya ƙirƙirar ayyukan yi maimakon dogaro da neman aikin yi.
Da yake jawabi a madadin kwamitin, shugabansa, Chief Leonard Nzadon, ya gode wa Gwamna Fintiri bisa amincewar da ya nuna musu, tare da alƙawarin yin aiki tukuru domin cika burin da aka kafa kwalejin a kai.