Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojoji sun karyata batun dake yawo cewa an sace malaman addini a...

Sojoji sun karyata batun dake yawo cewa an sace malaman addini a Zamfara

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa wasu malaman addinin Musulunci sun fada hannun ’yan bindiga a gidan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata, Abdul’aziz Abubakar Yari.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wasu mutane sun shiga hannun masu garkuwa da mutane yayin da suke kan hanyarsu daga yankin dajin Sububu da ke Karamar Hukumar Bakura zuwa garin Talata Mafara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji a 8 Division/Sector 2, Operation Fansa Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar ranar Lahadi, 13 ga watan Satumban 2026.

Rundunar ta bayyana rahotannin da ke cewa an sace malaman addinin a gidan Sanata Yari a matsayin ƙarya da kuma bayanin da bai yi daidai da gaskiyar abin da ya faru ba.

A cewar Laftanar Kanal Osoba, bayanan sirri da rundunar ta samu sun nuna cewa mutanen sun fada hannun masu garkuwa da mutane ne a lokacin da suke tafiya daga yankin dajin Sububu da ke Karamar Hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.

Ya jaddada cewa babu wani malamin addini da aka yi garkuwa da shi a gidan Sanata Abdul’aziz Yari, yana mai kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gano inda mutanen da aka sace suke tare da ceto su cikin koshin lafiya.

Ta ce an ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro a yankin, tare da amfani da bayanan sirri da kuma haɗin kan al’ummomin da ke yankunan domin gano masu aikata laifukan.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu sassan Jihar Zamfara ke ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro, musamman hare-haren ’yan bindiga da kuma sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Rundunar ta shawarci jama’a da su guji yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da su ba, tana mai cewa irin waɗannan bayanai na iya haifar da fargaba tare da kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro.

Haka kuma, ta buƙaci mazauna yankin da shugabannin al’umma su kasance cikin taka-tsantsan tare da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa ƙoƙarin da ake yi na ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Rundunar ta tabbatar da cewa Hedikwatar 8 Division da Sector 2 na Operation Fansan Yamma za su ci gaba da aiki tukuru wajen kare rayuka da dukiyoyin fararen hula tare da yaƙar miyagun laifuka a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments