Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dokoki ta dauki mataki game da harin kyamar baki a Afrika...

Majalisar Dokoki ta dauki mataki game da harin kyamar baki a Afrika ta Kudu

An dauki matakin ne saboda ci gaba da kai wa ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka hare-haren ƙyamar baki.

Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da dukkan ziyarar aiki zuwa Afrika ta Kudu, tare da umartar ’yan majalisar da su kaurace wa duk wani taron majalisa da wannan ƙasa ta shirya ko ta dauki nauyin gudanarwa har sai baba-ta-gani.

An dauki matakin ne sakamakon hare-haren ƙyamar baki da ake ci gaba da kai wa ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka a Afirka ta Kudu.

Shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun nuna damuwa kan rahotannin cewa ana kashe ’yan Najeriya, raunata su, korar su daga muhallansu tare da tilasta musu barin sana’o’insu, jarin da suka zuba, gidaje da sauran kadarorinsu a Afrika ta Kudu.

A cikin wata sanarwa da Magatakardar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Kamoru Ogunlana, ya sanya wa hannu, shugabannin majalisar sun ce hare-haren sun ci gaba duk da kiraye-kirayen da gwamnatin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki suka yi ga hukumomin Afrika ta Kudu da su dauki matakan da suka dace domin kare ’yan Najeriya da sauran ’yan kasashen waje.

Majalisar ta kuma amince da matakan da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki suka dauka wajen taimaka wa ’yan Najeriya da abin ya shafa da kuma sauƙaƙa fitar da wasu ’yan Najeriya daga Afrika ta Kudu.

A karkashin sabon matakin, an dakatar da dukkan ziyarar aiki zuwa Afrika ta Kudu da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, kwamitocinta, ’yan majalisa, jami’ai da ma’aikatanta ke yi.

Kauracewar ta kuma shafi tarukan karawa juna sani, bita, tarukan majalisa, musayar ra’ayoyi tsakanin majalisu da sauran ayyukan da hukumomin majalisar Afrika ta Kudu suka shirya ko suka dauki nauyin gudanarwa.

Majalisar ta kuma umarci ’yan majalisa da jami’anta da kada su halarci irin wadannan shirye-shirye da Afrika ta Kudu ta shirya, ko a zahiri ko ta kafar sadarwa.

An umarci Magatakardar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ya sanar da sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai, kwamitoci, sassa da dukkan jami’ai da ma’aikata game da matakin domin tabbatar da bin umarnin.

Sai dai majalisar ta jaddada cewa matakin ba wai yana nufin lalata kyakkyawar alakar tarihi, diflomasiyya da alakar jama’a tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu ba ne.

Ta ce matakin na nuna damuwa ne kan tsaro, mutunci da jin dadin ’yan Najeriya da ke zaune tare da gudanar da halastattun harkokin kasuwanci a Afirka ta Kudu.

Majalisar ta yi kira ga gwamnatin Afrika ta Kudu da ta dauki matakan gaggawa da za su kare ’yan Najeriya da sauran ’yan Afrika, tare da hana sake faruwar hare-haren ƙyamar baki.

Ta kuma bukaci a gudanar da bincike kan rahotannin hare-haren, a kama wadanda ake zargi tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Haka kuma, ta shawarci shugabannin majalisun dokokin jihohi da su lura da wannan mataki tare da duba yiwuwar daukar irin wannan mataki.

Shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ce za su ci gaba da sanya ido kan abubuwan da suka shafi tsaro da jin dadin ’yan Najeriya a Afrika ta Kudu.

Sun kara da cewa dakatarwar da kauracewar za su ci gaba da aiki har sai an ba da wani sabon umarni, kuma za a iya sake duba matakin idan yanayi ya canza.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments