Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta fara ɗaukar ma’aikatan wucin gadi da za su yi aikin babban zaɓen 2027.
Hukumar ta ce wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa INEC ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikata da horas da su domin zaɓen 2027, ba gaskiya ba ne.
INEC ta bayyana cewa shafin da ake yaɗawa ba shafin ɗaukar ma’aikata na hukuma ba ne, tare da gargadin jama’a da kada su shigar da bayanan sirri, su ɗora takardu ko kuma su biya kuɗi ta shafin.
Hukumar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan da irin waɗannan shafukan bogi, tare da tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin bin wata hanyar intanet da ake yaɗawa da sunan INEC.
INEC ta ce duk wata sanarwa da ta shafi ɗaukar ma’aikata ko wasu shirye-shiryen zaɓen 2027 za ta fito ne ta hanyoyin sadarwa na hukuma na hukumar.