Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta gano wani yunkurin kutsawa cikin asusun ta na X ba tare da izini ba, lamarin da ta bayyana a matsayin wata matsalar tsaro ta yanar gizo.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026, bayan an fara ganin shafin rundunar yana wallafa wasu saƙonni da suka shafi memecoin da misalin ƙarfe 3:50 na yamma.
Mukaddashiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojin Najeriya, Appolonia Anele, ta ce rundunar ta gano lamarin kuma nan take ta fara ɗaukar matakan fasaha da na tsaro domin kare asusun.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook na rundunar, Anele ta ce an ɗauki matakan da suka dace domin hana masu kutse sake samun damar shiga shafin tare da tabbatar da sahihancin bayanan da rundunar ke wallafawa.
Ta ce rundunar na aiki don tabbatar da cikakken tsaron asusun da kuma dawo da ikon gudanar da shi ga jami’an da aka ba izini.
Rundunar ta kuma gargadi jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi taka-tsantsan, tare da yin watsi da duk wani saƙo da ya bayyana a shafin X ɗin da ba a tabbatar da sahihancinsa ba.
Ta shawarci jama’a da su rika tabbatar da muhimman bayanai ta sauran kafafen sadarwa na hukuma na rundunar har sai an warware matsalar gaba ɗaya.
Har zuwa lokacin fitar da rahoton, ba a tabbatar da ko Rundunar Sojin Najeriya ta sake kwato cikakken iko kan asusun nata na X ba.
Wannan lamari ya faru ne kimanin makonni biyu bayan da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa an samu kutse cikin shafinta na X.
A ranar 15 ga Agusta, Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Samaila Uba, ya ce DHQ ta ɗauki matakan fasaha da suka dace domin kare asusun da kuma hana sake samun damar shiga ba tare da izini ba.
Abubuwan da suka faru sun ƙara jaddada muhimmancin ƙarfafa tsaron yanar gizo na kafafen sadarwar hukumomin tsaro, musamman waɗanda ake amfani da su wajen isar da muhimman bayanai ga jama’a.