Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiShirin gwamnati na rage kuɗin sufuri ba zai amfanemu a ƙauyuka ba...

Shirin gwamnati na rage kuɗin sufuri ba zai amfanemu a ƙauyuka ba — ‘Yan Najeriya

Miliyoyin ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tsadar sufuri tun bayan cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga iyalai.

Miliyoyin ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tsadar sufuri tun bayan cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga iyalai.

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin rage kuɗin sufuri daga ranar 1 ga Oktoba ta hanyar amfani da motocin CNG da masu amfani da wutar lantarki.

Sai dai wasu ‘yan Najeriya na nuna shakku kan shirin, musamman mazauna ƙauyuka, inda suke ganin motocin CNG da na lantarki ba za su magance matsalar sufuri a yankunan karkara ba.

A cikin shirin Nigeria Daily, an duba ko sabon alkawarin gwamnatin zai kawo sauƙin da ‘yan Najeriya ke fata, ko kuma zai kasance wani alkawarin da ya zo a daidai lokacin kamfen ɗin zaɓen 2027.

Haka kuma, an tattauna dalilin da ya sa matakin rage kuɗin sufuri ya ɗauki sama da shekaru uku bayan cire tallafin man fetur kafin a fara aiwatar da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments