Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai’Yar Najeriya ta lashe kyautar Naira miliyan 120 a gasar Alƙur’ani ta...

’Yar Najeriya ta lashe kyautar Naira miliyan 120 a gasar Alƙur’ani ta Saudiyya

Wata ’yar Najeriya, Maryam Danazimi Ibrahim, ta samu babban matsayi a gasar karatun Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a ƙasar Saudiyya, inda ta lashe kyautar Riyal 300,000, wanda ya yi daidai da kusan Naira miliyan 120.

Maryam ta zo ta farko a rukunin mata na haddar Alƙur’ani Izu 60 tare da Tafsiri, a gasar King Abdulaziz International Qur’an Competition ta 46.

’Yar asalin jihar Gombe ta yi fice wajen haddar Alƙur’ani gaba ɗaya, ingantaccen karatu, bin ƙa’idojin Tajweed da kuma fahimtar Tafsiri.

An bayyana Maryam a matsayin ɗaya daga cikin ’yan takara 50 da suka yi nasara a rukunai daban-daban na gasar, inda maza 25 da mata 25 suka samu kyaututtuka.

Nasarar ta ƙara ɗaukaka sunan Najeriya a fagen gasar Alƙur’ani ta duniya, yayin da Saudiyya ta bai wa waɗanda suka yi nasara kyaututtuka da jimillar darajarsu ta kai Riyal miliyan 10.26.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments