Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwankwaso ya miƙa rahoton sulhun ’yan takarar NDC na jihohin Arewa

Kwankwaso ya miƙa rahoton sulhun ’yan takarar NDC na jihohin Arewa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya miƙa wa Jagoran Jam’iyyar NDC na Ƙasa, Sanata Seriake Dickson, rahoton kammala aikin sulhu da daidaita ’yan takarar jam’iyyar a jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Abuja.

A cewar wani saƙo da mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, aikin sulhun ya kammala ne a yau Alhamis, 20 ga Agusta 2026.

Bayan kammala aikin, an miƙa rahoton tare da sunayen ’yan takarar ga Seriake Dickson domin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace a ƙarƙashin jam’iyyar.

Kwankwaso ya kuma yaba wa jagorancin jam’iyyar, NWC da dukkan ’yan takarar bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar wajen ganin an kammala aikin cikin nasara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments