Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bayyana matakan da zai dauka domin magance matsalar rashin tsaro idan aka zabe shi.
Atiku ya ce zai mayar da hankali ne kan karfafa jami’an tsaro, samar musu da isassun kayan aiki da kuma inganta tsarin jagoranci a hukumomin tsaron kasar.
Ya bayyana cewa cikin kwanaki 100 na farko da zai fara mulki, zai kara yawan jami’an tsaro tare da tabbatar da cewa sun samu kayan aikin da za su taimaka musu wajen dakile hare-haren ta’addanci da sauran laifukan da suka addabi sassan Najeriya.
A cewarsa, matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar na da alaka da gazawar shugabanci, yana mai cewa akwai bukatar shugabannin hukumomin tsaro su dauki cikakken alhaki wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Atiku ya kuma yi magana kan kalubalen da jami’an tsaro da tsofaffin sojoji ke fuskanta, inda ya ce ya kamata a tabbatar da cewa jami’an tsaro sun samu hakkokinsu da kuma kayan aiki na zamani.
Baya ga batun tsaro, Atiku ya sake bayyana aniyarsa ta dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaben shugaban kasa na 2027.
Ya ce cire tallafin bai kawo saukin rayuwa ga ‘yan Najeriya kamar yadda ake tsammani ba.
Sai dai ya ce idan ya sha kaye a zaben 2027, ba zai sake neman takarar shugaban kasar Najeriya ba.