Fadar Shugaban Ƙasa ta soki shirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce dawo da tallafin man fetur bai dace da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu ba.
Onanuga ya bayyana cewa komawar tallafin zai sake ɗora wa gwamnati nauyin biyan tazarar da ke tsakanin farashin man fetur da kuɗin da ake kashewa wajen samar da shi. Ya ce hakan na iya ƙara yawan bashin gwamnati tare da rage kuɗaɗen da za a iya warewa ayyukan raya ƙasa.
Ya kuma ce tun bayan cire tallafin, harkar tace man fetur a cikin gida ta samu ci gaba, musamman saboda ƙara samar da fetur da matatun mai na cikin gida ke yi.
Gwamnati kuma ta bayyana CNG a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin rage tsadar makamashi ga ’yan Najeriya.