Akalla sojoji huɗu ake fargabar sun rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari garin Kebbe, da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto, ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce maharan sun isa garin da misalin ƙarfe 10 na safe, dauke da manyan makamai, sannan suka shiga yawo kafin daga bisani su far wa shaguna tare da kwashe wayoyin hannu, kayan abinci da man fetur.
Wani mazaunin garin ya ce ya ga sama da babura 200 da maharan suka zo da su.
An kuma ruwaito cewa maharan sun kai hari hedikwatar ’yan sandan yankin tare da shiga babban Asibitin Kebbe, inda suka lalata motar DPO da aka ajiye a harabar asibitin.
Sai dai babu rahoton kashe fararen hula ko jami’an ’yan sanda a hedikwatar.
Daga nan ne maharan suka kai hari wani sansanin sojoji da ke wajen garin, inda aka yi musayar wuta mai tsanani tsakaninsu da dakarun soji.