Ma’aikatan haƙar ma’adinai bakwai sun rasa rayukansu bayan wani ramin haƙa ya rufta a yankin Kassa da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Plateau.
Lamarin ya faru ne da yammacin Laraba, yayin da ma’aikatan ke gudanar da aikin haƙar ma’adinai a wurin.
Wani mazaunin yankin, Albert Danlami, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na dare, lokacin da ramin ya rufta ba zato ba tsammani kan ma’aikatan.
Ya ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun makale a ƙarƙashin ƙasa, lamarin da ya sa mazauna yankin da sauran ma’aikatan haƙar ma’adinai suka fara aikin ceto.
Sakataren yaɗa labarai na Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da mutuwar ma’aikatan bakwai.
Ya ce an yi ƙoƙarin ceto su bayan ruftawar ramin, amma daga bisani aka gano cewa duk sun mutu.
Ruftawar ramukan haƙar ma’adinai dai na ci gaba da haddasa asarar rayuka a wasu al’ummomin haƙar ma’adinai da ke Barkin Ladi, Jos South, Riyom da sauran ƙananan hukumomin Plateau.