Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce a halin yanzu abin da al’ummar Jihar Kano suka fi buƙata shi ne magance matsalar ƙarancin ruwan sha, maimakon mayar da hankali kan shirin auren gata.
Kwankwaso ya bayyana cewa matsalar ruwan sha na jefa al’umma cikin wahala, don haka ya kamata gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali wajen samar da ingantaccen ruwa ga jama’a.
A cewarsa, ya dace a magance muhimman matsalolin da ke addabar al’umma kafin kashe makudan kuɗaɗe kan wasu shirye-shirye.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da Gwamnatin Jihar Kano ke ci gaba da aiwatar da shirin auren gata, wanda aka ware wa kuɗaɗe domin tallafa wa ma’auratan.
Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta fifita abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum, musamman samar da ruwa, tare da ɗaukar matakan da za su rage wa al’umma wahalhalun da suke fuskanta.