Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya rayuwar almubazzaranci kamar yadda wasu ke zargi.
Adedeji ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels Television, yayin da yake magana kan salon rayuwar shugabannin gwamnati a lokacin da ’yan Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.
A cewarsa, Tinubu wani lokaci kan yi tafiya daga gidansa zuwa ofis da ƙafa, yayin da yake amfani da mota ne musamman idan zai je filin jirgin sama. Ya kuma ce shugaban ƙasar kan ci abinci sau ɗaya kacal a rana.
Adedeji ya ƙara da cewa Tinubu bai fita daga Najeriya ba a cikin ’yan watannin da suka gabata. Da aka tambaye shi kan motocin alfarma da ke cikin ayarin shugaban ƙasar, ya ce bai kamata a ɗauki mallakarsu a matsayin almubazzaranci ba, domin shugaban yana da ikon mallakar irin waɗannan motoci.
Kalaman shugaban NRS na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan kashe-kashen gwamnati da salon rayuwar shugabannin siyasa, musamman a lokacin da ’yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki.