Tsohon Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC, Timi Frank, ya zargi tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, da ci gaba da amfani da sunan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wajen jawo hankalin jama’a duk lokacin da zaɓe ya gabato. Ya ce wannan salon ya tsufa kuma ba zai ƙara yaudarar ’yan Najeriya ba.
Frank ya bayyana haka ne a martaninsa ga kalaman Obasanjo, inda ya ce tsohon shugaban ƙasar na yawan ɗora wa Atiku alhakin matsalolin siyasa maimakon mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa.
Ya kuma yi zargin cewa Obasanjo na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a ta hanyar ci gaba da sukar Atiku, yana mai cewa hakan ba zai sauya ra’ayin ’yan Najeriya ba kan makomar siyasar ƙasar.
Timi Frank ya buƙaci Obasanjo ya daina abin da ya kira “yaƙin neman ɓata suna” kan Atiku, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan samar da mafita ga matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar Najeriya.
Ya ce ’yan Najeriya za su yanke hukunci bisa abin da suka gani da suka fuskanta, ba wai ta hanyar zarge-zarge ko yaƙin neman ɓata suna ba, yana mai cewa makomar siyasar 2027 za ta kasance hannun masu kaɗa ƙuri’a.