Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiNCAA: Kasa da mutane miliyan ɗaya ne kawai ke yawan hawa jirgin...

NCAA: Kasa da mutane miliyan ɗaya ne kawai ke yawan hawa jirgin sama a Najeriya

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayyana cewa duk da ana sayar da tikitin jiragen sama kusan miliyan 14 a duk shekara a zirga-zirgar cikin gida, adadin ƴan Najeriya da ke amfani da jirgin sama akai-akai bai kai mutum miliyan ɗaya ba.

Daraktan kula da ingancin jiragen sama na hukumar, Godwin Balang, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi kan halin da fannin sufurin jiragen sama ke ciki.

A cewarsa, yawan tikitin da ake sayarwa ba yana nufin mutane miliyan 14 ne ke hawa jirgi ba, domin mutum guda na iya sayen tikiti sau da dama cikin shekara saboda tafiye-tafiyensa.

Balang ya ce hakan na nuna cewa har yanzu zirga-zirgar jiragen sama ba ta zama hanyar sufuri da mafi yawan ƴan Najeriya ke amfani da ita ba, inda ya jaddada buƙatar samar da sauƙin farashin tikiti da inganta ayyukan jiragen sama domin jawo ƙarin matafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments