Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bukaci duk masu niyyar gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 da su fara biyan kafin alkalami na N5m domin tabbatar da gurabensu tun da wuri.
Hukumar ta bayyana cewa tsarin biyan kuɗin a matakai zai sauƙaƙa wa maniyyata nauyin biyan kuɗin Hajji gaba ɗaya lokaci guda, tare da ba su damar kammala biyan kuɗin cikin sauƙi kafin lokacin tafiya.
NAHCON ta ƙara da cewa fara biyan kuɗin da wuri zai taimaka mata wajen tsara masauki, sufuri, da sauran muhimman shirye-shiryen da suka shafi aikin Hajji cikin lokaci da inganci.
Hukumar ta yi kira ga duk masu niyyar zuwa Hajjin 2027 da su yi amfani da wannan dama domin gujewa cunkoso da matsalolin shirye-shiryen ƙarshe.