Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, murnar cika shekaru 65 da haihuwa.
A cikin saƙon taya murnar da ya wallafa, gwamnan ya bayyana Sarkin a matsayin shugaba mai hangen nesa, mai hikima da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma.
Ya ce irin gudummawar da Mai Martaba ke bayarwa wajen bunƙasa ilimi, tattalin arziki, da kyawawan dabi’u na ci gaba da zama abin koyi ga al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Sarkin lafiya, tsawon rai, hikima da basira, tare da ba shi ikon ci gaba da jagorantar Masarautar Kano cikin adalci da nasara.