Likitan da ke kula da lafiyar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Bello Abubakar, ya musanta zargin da Hukumar ICPC ke yi masa na fitar da rahoton lafiya na bogi.
A cikin bayanin da ya gabatar, ya ce shi ne ya rubuta rahoton lafiyar Nasir El-Rufa’i, amma ya jaddada cewa bai san Mohammed Bala Aliyu, wanda ake zargin ya yi amfani da rahoton wajen rantsuwar kotu ba.
Dr. Abubakar ya kuma bayyana cewa ya dade yana kula da lafiyar El-Rufa’i tun daga shekarar 2005, yana mai cewa duk abin da ya yi ya kasance bisa ƙa’idar aikin likitanci.
Sai dai ICPC na ci gaba da zarginsa da samar da rahoton da ake ikirarin an yi amfani da shi wajen neman belin El-Rufa’i, lamarin da ke gaban hukumomin da abin ya shafa.