Rundunar ’yan sanda ta cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a mutuwar Ibrahim Mbaye, ɗalibin Jami’ar Jos, bayan an zarge shi da satar waya.
Rahotanni sun ce waɗanda ake zargin sun ɗaure shi tare da yi masa mugun duka da katako da bulalai domin tilasta masa ya bayyana inda wayar da ake zargin ya sata take. Sai dai daga bisani ya rasa ransa sakamakon raunukan da ya samu.
Bidiyon da ya nuna yadda aka azabtar da marigayin ya bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a tare da haifar da kiraye-kirayen a tabbatar da adalci.
A halin yanzu, rundunar ’yan sanda ta ce tana ci gaba da bincike, yayin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ke kira da a gurfanar da duk masu hannu a lamarin gaban kotu.