Gwamnatin Jihar Adamawa ta ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa samar da wutar lantarki ta hasken rana, inda Ma’aikatar Ayyuka da Bunƙasa Makamashi, tare da haɗin gwiwar Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Ƙauyuka (REA), suka duba ayyukan gina wasu ƙananan tashoshin wutar lantarki a yankunan karkara daban-daban na jihar.
Tawagar da Daraktan Watsa Wuta, Rarrabawa da Samar da Wutar Lantarki a Ƙauyuka, Injiniya James Yohanna, ya jagoranta, ta duba wuraren aikin da ke Kuva Gaya, Kwakwaah, Ga’anda da Shuwa, da kuma Babban Asibitin Michika da wani Asibitin Kula da Lafiya na Farko.
A yayin ziyarar, injiniyoyin sun tabbatar da cewa muhimman sassan ayyukan, ciki har da shimfiɗa wayoyin lantarki, na’urorin auna amfani da wuta da sauran kayan aikin da ake buƙata, sun kusa kammala.
Jami’an sun bayyana gamsuwarsu da yadda ayyukan ke tafiya, tare da cewa ana gudanar da su bisa ƙa’idojin fasaha da inganci da aka amince da su.
Sun ce shirin samar da wutar lantarki ta hasken rana na da nufin samar da tsaftatacciyar wuta mai ɗorewa da inganci ga al’ummomin karkara da ba su da isasshen wutar lantarki, tare da inganta wutar da ake amfani da ita a gidaje, asibitoci, makarantu da ƙananan sana’o’i.
Mazauna yankunan da za su amfana da ayyukan sun yaba wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da Hukumar REA, inda suka bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki da zai inganta rayuwarsu, haɓaka harkokin tattalin arziki da samar da ingantacciyar rayuwa a yankunan karkara.