Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa Sufeto Janar na ’Yan Sanda (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya umarci jami’an ’yan sanda su rika harbin masu laifi kai tsaye.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an yi wa kalaman IGP da ya yi a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Makurdi, Jihar Benue, mummunar fassara a wasu kafafen yaɗa labarai.
Rundunar ta bayyana cewa abin da Sufeto Janar ya yi shi ne tunatar da jami’an ’yan sanda tanade-tanaden doka da ƙa’idojin aiki da ke bayyana yanayin da jami’i zai iya amfani da bindiga bisa doka.
Ta ƙara da cewa IGP ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin amfani da makamai, tare da bayyana cewa bai ba da wani sabon umarni na harbin masu laifi ba tare da bin tanadin doka da ƙa’idojin aikin ’yan sanda ba.