Dakarun kawancen sojojin Saudiyya sun kai zafafan hare-hare ta sama kan wasu wuraren da mayakan Houthi ke amfani da su, a wani mataki da aka ce na da nufin rage barazanar da ƙungiyar ke haifarwa ga tsaron yankin.
A cewar sanarwar da babban gidan talabijin na masarautar Saudiyya ya fitar, hare-haren sun lalata wuraren soji da ake zargin mayakan Houthi ke amfani da su wajen kai hare-hare da kuma barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci a yankin.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, mayakan Houthi ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan hare-haren da Saudiyya ta kai ba.